logo

HAUSA

Sin ta bukaci Amurka da ta martaba alkawarin da ta dauka game da ka'idar “kasar Sin daya tak a duniya”

2022-09-28 20:18:39 CMG Hausa

              

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bukaci kasar Amurka da ta mutunta alkawarin da ta yi game da manufar “kasar Sin daya tak a duniya” cikin sauki ba tare da wata rufa-rufa ba.

Wang ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labaran da aka saba shiryawa, lokacin da yake tsokaci kan kalaman da mataimakiyar shugaban kasar Amurka Kamala Harris ta yi a safiyar yau cewa, Amurka za ta ci gaba da zurfafa dangantakar da ba ta shafi aiki ba da yankin Taiwan na kasar Sin

Wang ya ce, Harris ta kuma furta yayin da ta kai ziyara kasar Japan cewa, wai kasar Sin ba ta daukar muhimman abubuwa na tsarin dokokin kasa da kasa da muhimmanci. Yana mai cewa, duk da kalaman Madam Harris ta yi kan kasar Sin, kasar Amurka ce mai ruguza tsarin kasa da kasa.

Ya bayyana cewa, Amurka ta amince karara a cikin sarwoyin hadin gwiwa guda uku da kasashen Sin da Amurka suka cimma cewa, kasar Sin daya ce tak a duniya, kuma Taiwan wani bangare ne na kasar Sin, kuma sun amince da gwamnatin jamhuriyar jama'ar kasar Sin a matsayin halaltacciyar gwamnatin kasar Sin.

 

Wang ya kara da cewa, martaba kalaman da mutum ya furta, ita ce ka’ida mafi mahimmanci. Yana mai cewa, idan har bangaren Amurka bai mutunta alkawuran da ya dauka ba, ta yaya ya cancanci yin magana kan dokoki? Zai zama mai lalata dokokin kasa da kasa ne kawai.(Ibrahim)