logo

HAUSA

Babban bankin Nijeriya ya kara kudin ruwa zuwa kaso 15.5

2022-09-28 10:41:22 CMG HAUSA

 

Babban bankin Nijeriya ya sanar da kara kudin ruwa, daga kaso 14 zuwa 15.5 yayin da ake tsaka da fuskantar hauhawar farashin kayayyaki.

Gwamnan babban bankin Nijeriya, Godwin Emefiele ne ya sanar da hakan ga manema labarai bayan kammala taron kwamitin kula da manufofin kudi na bankin wanda ya gudana jiya, a Abuja.

A cewar gwamnan, babban bankin ya kara kudin ruwan ne domin dakile hauhawar farashin kayayyaki a kasar mafi yawan al’umma a Afrika. (Fa’iza Mustapha)