logo

HAUSA

Wani hari a Burkina Faso ya yi sanadin mutuwar sojoji 11 da batar fararen hula 50

2022-09-28 11:17:01 CMG HAUSA

 

Gwamnatin kasar Burkina Faso, ta sanar da cewa, sojoji 11 sun mutu, yayin wani hari da aka kai wa wani jerin gwanon motoci dauke da kayayyaki, ranar Litinin, a yankin arewacin kasar.

A cewar sanarwar da gwamnatin ta fitar jiya, ’yan ta’adda sun kai hari kan wani jerin gwanon motocin kayayyaki da sojoji ke yi wa rakiya. Motocin na kan hanyarsu ne ta zuwa birnin Djibo, a lokacin da aka kai musu hari a kusa da garin Gaskinde dake lardin Soum.

Rahotannin na wucin gadi sun bayyana cewa, sojoji 11 sun mutu, wasu mutane 28 sun jikkata, cikinsu kuma akwai sojoji 20. Har ila yau, kimanin fararen hula 50 sun bata.

Sanarwar ta kara da cewa, harin ya haifar da asara mai yawa. Kuma yanzu haka ana farautar maharan. (Fa’iza Mustapha)