logo

HAUSA

An yi bikin murnar ranar kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin a Habasha

2022-09-28 11:25:11 CMG HAUSA

 


An gudanar da wani biki na musammam a birnin Addis Ababa na Habasha, domin murnar bikin cika shekaru 73 da kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin.

Bikin wanda aka yi a zahiri da kuma ta kafar intanet a ranar Litinin, ya samu halartar jami’an gwamnatin Habasha da jami’an diflomasiyya dake Habashar da wakilan ’yan kasuwa da malamai. Akwai kuma wakilan kamfanonin kasar Sin da na tawagar jami’an lafiya ta kasar Sin da na cibiyar Confucius.

Tsohon shugaban Habasha Mulatu Teshome, ya bayyana a jawabinsa cewa, tun bayan kafuwar Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin, kasar ta yi ta samun ci gaban da ya kai ta matsayin kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, haka kuma rayuwar jama’arta ta ingantu kwarai.

Ya kuma yabawa muhimmiyar dangantaka da hadin gwiwar dake ci gaba da fadada tsakanin kasashen biyu, da kuma dimbin gudunmawar da Sin ta bayar ga huldarta da Habasha.

A nasa jawabi, jakadan Sin a Habasha, Zhao Zhiyuan, ya ce dangantakar kasashen biyu a nan gaba na da haske da kuma tarin damarmaki. Ya kuma jaddada cewa, kasashen biyu na da buri guda na kyautata rayuwar jama’arsu. (Fa’iza Mustapha)