logo

HAUSA

Kasar Sin na ci gaba da taka muhimmiyar rawa da al'ummar duniya kan batun Ukraine

2022-09-28 19:49:37 CMG Hausa

 

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana cewa, matsayin kasar Sin game da batun kasar Ukraine, yana nan daram kuma bai sauya ba. Wang ya bayyana hakan ne yayin taron manema labaran da aka saba shiryawa Larabar nan, yayin da yake amsa tambayar da aka yi masa kan wasu yankuna 4 na kasar Ukraine, da suka kada kuri'ar neman hadewa da kasar Rasha.

Wang ya nanata cewa, har kullum kasar Sin tana bayyana cewa, ya kamata a mutunta ikon mulkin kasa da cikakkun yankunan dukkan kasashe, da kiyaye manufofi da ka'idojin kundin tsarin mulkin MDD, da daukar kwararan matakan tsaro na dukkan bangarori da muhimmanci, da kokarin goyon bayan warware rikici cikin lumana.

Ya kara da cewa, kasar Sin tana goyon bayan zaman lafiya, kuma za ta ci gaba da taka rawar da ta dace tare da kasashen duniya game da batun kasar Ukraine.(Ibrahim)