logo

HAUSA

Kamfanin Sin na taimaka wajen gina “Kusurwar kasar Sin” a Abujan Najeriya

2022-09-27 10:35:07 CMG Hausa

An gudanar da bikin bude “Kusurwar kasar Sin” a makarantar gwamnati dake gunduma ta 11 a birnin Abuja, fadar mulkin tarayyar Najeriya, wanda rukunin kamfanin CRCC na kasar Sin reshen Najeriya ya gyara a safiyar ranar 23 ga wata. Bikin ya samu halartar karamin jakadan kasar Sin dake Najeriya Zhang Yi, da darektan cibiyar yada al’adun kasar Sin a kasar Li Xuda, da manajan kamfanin CRCC reshen Najeriya Wan Lianyu, da shugaban hukumar ba da ilmi a matakin farko ta birnin Abuja Alhassan Sule, da wakilan kungiyar malamai da dalibai na makarantar da wasu manema labarai.

A jawabinsa yayin bikin, karamin jakadan kasar Sin dake Najeriya Zhang Yi ya bayyana cewa, aikin ba da ilmi shi ne tushen ci gaban kasa, don haka, ofishin jakadancin kasar Sin yana ba da muhimmanci ga cudanyar ba da ilmi dake tsakanin Sin da Najeriya, haka kuma ya dade yana hada kai tare da kamfanonin kasar Sin dake Najeriya, domin raya aikin ba da ilmi a kasar.

A nasa bangare, shugaban hukumar ba da ilmi a matakin farko ta birnin Abuja Alhassan Sule, ya godewa ofishin jakadancin kasar Sin da kamfanonin kasar Sin dake Najeriya, bisa kokarinsu na inganta yanayin makarantun kasar, da samar da tallafin kudi ga dalibai masu karamin karfi. haka kuma ya yaba da aikin gyara makaranta da kamfanonin kasar Sin suke yi. Yana mai cewa, nan gaba makarantar za ta kare sabbin kayayaykin da aka samar musu, tare kuma da yada al’adun kasar Sin a kasar yadda ya kamata. (Jamila)