logo

HAUSA

Shitu Yusuf Aliyu: Harshen Sinanci ya burge ni matuka

2022-09-27 15:10:01 CMG Hausa

Shitu Yusuf Aliyu, matashi ne dan asalin jihar Kano dake arewacin Najeriya, wanda ya taba koyon harshen Sinanci, a makarantar koyar da yaren Sin dake garin Kwankwaso na karamar hukumar Madubin Kano.

A zantawar da Murtala Zhang ya yi da shi, malam Shitu ya bayyana dalilin da ya sa ya yi sha’awar koyon yaren Sinanci, da abubuwa da dama da suka burge shi game da wannan yare. Har ma ya nuna fahimtarsa kan al’adun kasar Sin.

A karshe, malam Shitu Aliyu ya kuma bayyana babban burin da yake kokarin cimmawa. (Murtala Zhang)