Sin tana kawo tabbaci ga duniya yayin da take cikin yanayi na tangal-tangal
2022-09-27 10:06:52 CMG Hausa
Yanzu haka kasashen duniya suna cikin yanayi mai sarkakiya, kuma ba a kai ga shawo kan annobar cutar COVID-19 ba tukuna, kana tattalin arzikin duniya yana kara fuskantar koma baya, baya ga matsalar karancin makamashi da hatsi sakamakon tsananta rikicin Ukraine. A hannu guda kuma tunanin yakin cacar baki, da siyasar nuna fin karfi, da ra’ayin bangaranci da kare moriyar kashin kai, sun sake bulla a fadin duniya.
A game da wannan batu, a jawabin da ya gabatar yayin taron muhawara na babban taron MDD karo na 77, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya sake yin bayani kan shawarwarin tabbatar da tsaron duniya da raya duniya da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, inda ya zayyana manufofi shida, wadanda suke tabbatar da wanzar da zaman lafiya a maimakon rikici, da raya kasa a maimakon talauci, da bude kofa ga ketare a maimakon rufe kofa, da gudanar da hadin gwiwa a maimakon nuna kiyayya, da hada kai a maimakon kawo baraka, da tabbatar da adalci a maimakon nuna fin karfi, manufofin dake nuna matsayin kasar Sin game da muhimman batutuwan da suka shafi harkokin kasa da kasa.
Shugaban babban taron MDD karo na 77 Korosi Csaba, ya yi nuni da cewa, kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa a harkokin kasa da kasa, kuma muhimman shawarwarin da shugaba Xi Jinping ya gabatar, su ma sun samar da dabarun daidaita kalubalolin da kasashen duniya ke fuskanta a halin da ake ciki yanzu.
Shi ma babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yaba wa muhimmiyar rawar da kasar Sin da dade tana takawa, wajen goyon bayan manufar tafiyar da harkokin kasa da kasa tsakanin bangarori daban daban, da ingiza hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa, da samun dauwamammen ci gaba da sauransu. Yana mai bayyana cewa, MDD tana goyon bayan shawarar raya kasashen duniya baki daya da shugaba Xi ya gabatar, yana mai cike da imani cewa, shawarar za ta taimakawa yunkurin samun dauwamammen ci gaban duniya nan da shekarar 2030.
Duk da cewa, kalulabe da kasashen duniya suke fuskanta, kasar Sin tana taka muhimmiyar rawar da ta dace don ganin kwalliya ta biya kudin sabulu. (Jamila)