logo

HAUSA

Kasar Sin ta bankado karin shaidu game da kutsen yanar gizo da Amurka ta yi mata

2022-09-27 16:00:27 CMG Hausa

Kasar Sin ta fitar da wani sabon rahoton bincike, wanda a cikinsa ta ce ta karo bankado wasu shaidu da ke nuna cewa, hukumar tsaro ta kasar Amurka (NSA) ce ke da hannu a "dubban kutsen yanar gizo" da aka yiwa wata jami'ar kasar Sin.

Rahoton ya ce, an gano cewa, wadannan kutsen intanet, an yi su ne daga ofishin hukumar Tailored Access Operation (TAO) mai alaka da NSA ta Amurka, lamarin da ya fallasa kura-kurai, da matakai marasa dacewa na hukumar yayin kutsen.

Rahoton ya yi cikakken bayani kan yadda kungiyar ta TAO ke yin kutse a cibiyar sadarwa ta wata jami'ar kasar Sin. Haka kuma tawagar binciken kasar Sin ta gano cewa, TAO ta kwafi wasu bayanan sirri na wasu muhimman mutane a babban yankin kasar Sin, aka kuma aika bayanan zuwa hedkwatar NSA ta hanyar wasu nau’rorin tattara bayanai.

Rahoton ya ce, an gano hakikanin wadanda suka yi wannan kutse su 13.

Rahoton ya kuma yi cikakkun bayanai game da kutsen yanar gizon da Amurka ta yiwa jami'ar kasar Sin, domin za ma darasi ga kasashen duniya, ta yadda za su iya ganowa da dakile kusten yanar daga kungiyar TAO ta Amurka. (Ibrahim)