logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi nasarar harbar tauraron dan Adam na gwaji mai lamba 16 A/B da tauraron dan adam na gwaji mai lamba 17

2022-09-27 13:15:15 CMG Hausa

Da karfe 8 saura mituna 10 na safiyar yau ne, kasar Sin ta yi nasarar harba taurarin dan Adam na gwaji mai lamba 16 A/B da kuma tauraron dan adam gwaji mai lamba 17, ta hanyar amfani da rokar Long March mai lamba 6 daga cibiyar harbar tauraron dan Adam ta Taiyuan, kuma taurarin dan Adam din sun shiga cikin falaki kamar yadda aka tsara, abin dake nuna cewa, aikin harba taurarin dan-Adam din ya yi nasara.

Galibi dai, ana amfani da wannan rukuni na taurarin dan Adam ne a lokacin da ake kidayar filayen yankunan kasa, da tsara shirin raya birane, da rigakafin aukuwar bala'u da rage radadi da sauransu.

Shi ne karo na 440 ke nan da aka yi amfani da rokar Long March, wajen harba taurarin dan-adam zuwa sararin samaniya. (Mai fassarawa: Safiyah Ma)