logo

HAUSA

Gwano Ba Ya Jin Warin Jikinsa

2022-09-27 21:41:43 CMG Hausa

Yau Talata 27 ga wata sashen kandagarkin kutsen na’ura mai kwakwalwa ta kasar Sin ko CVERC a takaice da kamfanin fasaha na Qihoo 360 sun kaddamar da rahoton bincike na biyu dangane da yadda aka yi kutse a na’urori masu kwakwalwa na jami’ar koyar da ilimin fasaha ta kasar Sin, ko Northwestern Polytechnical University, inda aka yi karin bayani kan yadda hukumar leken asiri ta Amurka ko NSA, ta yi amfani da wata kafa mai lakabin TAO wajen yin kutsen fiye da sau dubu guda. Ta haka an kara sanin yadda NSA take satar bayanai a yanar gizo. Gwano ba ya jin warin jikinsa. Kasar Amurka ba za ta iya musunta abin da ta aikata ba.

Hakika dai Amurka ta dade tana satar bayanai a yanar gizo a fili. Edward Snowden, tsohon ma’aikacin kamfanin da ya daddale kwangila da gwamnatin Amurka ya bayyana wa kafofin yada labaru a shekarar 2013 cewa, NSA tana leken asiri a duk fadin duniya a ko da yaushe. Rahoton da wani kamfanin yanar gizo na kasar Sin ya gabatar a bana ya nuna cewa, a cikin shekaru fiye da 10 da suka gabata, NSA ta yi kutse a na’urori masu kwakwalwa a wurare 403 da ke kasashe da yankuna 47 a duniya, ciki had da kasashen Sin, Birtaniya, Jamsu da Faransa.

Yayin da Amurka take satar bayanai bisa ga fasahar zamani, tana kuma mayar da kanta wadda aka yi wa kutsen, har ma ta hada hannu da kawayenta don shafa wa kasar Sin bakin fenti. Rahotannin kasar Sin sun taimakawa kasashen duniya kara sanin gaskiyar lamarin. (Tasallah Yuan)