logo

HAUSA

Xi Ya Jajantawa Putin Game Da Harin Bindigar Da Aka Kai Wata Makaranta A Rasha

2022-09-27 19:32:14 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon jaje ga takwaransa na Rasha, Vladimir Putin, game da harin bindiga da ya auku a wata makaranta a kasar.

Cikin sakon, shugaba Xi ya ce ya kadu da samun labarin harin bindigar a birnin Izhevsk na Rasha. Kuma a madadin gwamnati da al’ummar Sin da shi kansa, yana jimamin wadanda aka kashe yayin harin tare da jajantawa iyalansu.

Shi ma kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yau cewa, Sin na jajantawa iyalan wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata.

Mutane akalla 17, ciki har da dalibai 11 ne aka kashe yayin harin na ranar Lahadi. (Fa’iza Mustapha)