logo

HAUSA

Shugabancin JKS Ya Amfani Daukacin Al’ummun Duniya

2022-09-27 19:43:44 CMG Hausa

Shugaban jam’iyyar PCT mai mulkin kasar Congo (Brazzavile) Pierre Moussa, ya bayyana shugabancin jami’iyyar Kwaminis ta kasar Sin a matsayin wanda ya cimma nasarori kuma ya amfani daukacin al’ummun duniya.

Yayin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Pierre Moussa, ya ce shugabancin JKS ya tabbatar da ci gaba da nasarori a bangarori daban daban na rayuwar Sinawa, kuma ba su kadai suka amfana ba, har da sauran jama’ar duniya.

Ya ce yadda kasar Sin ta fatattaki talauci karkashin shugabancin JKS, gagarumin ci gaba ne, yana mai cewa, JKS ta cika alkawurran da ta yi wa Sinawa da jama’ar duniya.

Haka kuma, ya ce yana ganin babban taron wakilan JKS karo na 20 dake karatowa, na da matukar muhimmanci ga duniya, kuma yana mai fatan zai gudana cikin nasara. (Fa’iza Mustapha)