logo

HAUSA

Kusan kasashe 70 sun nuna rashin amincewarsu da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin

2022-09-27 11:51:37 CMG Hausa

Wasu rukunin kasashe sun jaddada rashin amincewarsu, a yayin zaman kwamitin kare hakkin dan-Adam na MDD karo na 51 da yanzu haka ke gudana a birnin Vienna, kan yadda wasu kasashe ke tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin. Suna masu cewa, batutuwan da suka shafi  Xinjiang, da Hong Kong da Tibet, harkokin cikin gida ne na kasar Sin, kuma bai kamata a rika siyasantar da batun hakkin dan Adam da nuna ma'aunai biyu ko tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin ta hanyar fakewa da batun kare hakkin dan Adam ba.

Wata sanarwar hadin gwiwa da kasar Pakistan ta gabatar a madadin kasashe 68, ta jaddada cewa, mutunta ikon mulki, da 'yancin kai da cikakkun yankuna da rashin tsoma baki a harkokin cikin gida na kasashe masu cin gashin kansu, na wakiltar muhimman ka'idojin da suka shafi dangantakar kasa da kasa.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, ya kamata dukkan bangarori, su martaba manufofi da ka'idojin yarjejeniyar MDD, da kiyaye ka'idojin kasa da kasa, da rashin nuna son kai, da nuna gaskiya da adalci, da mutunta 'yancin jama'ar kowace kasa na zabar hanyar samun ci gaba daidai da yanayin kasashensu.

Ta kara da cewa, ya kamata a kula da dukkan hakkokin bil-adama ba tare da nuna bambanci ba, da ba muhimmanci ga 'yancin tattalin arziki,da zamantakewa da al'adu da kuma musamman 'yancin ci gaba (Ibrahim).