logo

HAUSA

An kaddamar da kwamitin inganta tsaro da ci gaban yankin Sahel a MDD

2022-09-26 20:21:55 CMG Hausa

 

An kaddamar da wani kwamiti domin inganta tsaro da ci gaba a yankin Sahel, a ranar Asabar, a birnin New York, yayin wani taron manyan jami’ai kan yankin wanda ke fama da yaki, a gefen babban taron MDD na shekara-shekara .

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya ce shugabannin Afrika sun kaddamar da kwamitin ne domin nazarin yanayin yankin Sahel tare da gabatar da shawarwari kan hanyoyin da za a kyautata shigar kasashen duniya cikin batun da tsara yadda za a tunkari kalubale masu sarkakiya da yankin ke fuskanta.

Cikin jawabansu da aka wallafa a ranar Asabar, shugabannin sun bayyana kalubalen da yankin ke fuskanta, ciki har da karuwar rikicin masu tsattsauran ra’ayi da karuwar matsalolin tattalin arziki saboda sauyin yanayi da annobar COVID-19 da matsalolin siyasa.

Sun kuma yi kira da a hada karfi da karfe a matakan kasa da shiyyoyi da ma duniya, domin daidaita yanayin tsaro da na shugabanci da kalubalen ci gaba da ake fuskanta, da daukar dabaru bisa manufofin siyasa da za su mayar da hankali kan moriyar daukacin jama’a. (Fa’iza Mustapha)