logo

HAUSA

Fasinjoji miliyan 32 ne suka yi kai komo a filin tashi da saukar jiragen sama na Daxing cikin shekaru 3

2022-09-26 10:33:58 CMG Hausa

Yawan fasinjojin da suka tashi da ma sauka a filin jirgin sama na Beijing Daxing na kasar Sin, ya zarce miliyan 52 a cikin shekaru 3 da suka gabata.

Bayanai na nuna cewa, a cikin shekaru uku da suka gabata, filin jiragen saman na Daxing, ya kula da tan 370,000 na kaya da wasiku. Kuma jirage 450,000 ne suka tashi ko kuma suka sauka a filin jirgin.

A halin yanzu, kamfanonin jiragen sama 26 na cikin gida ne suke aiki a filin jirgin saman. Haka kuma filin jirgin saman, ya bude jimillar hanyoyin jiragen sama guda 266, tare da hada sassa 185.

A jiya ne dai, aka yi bikin cika shekaru uku da fara ayyuka a filin jirgin saman na Daxing. (Ibrahim)