logo

HAUSA

Kasar Amurka ce kan gaba wajen yada labarai marasa tushe

2022-09-26 20:30:22 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya yi tsokaci game da rahoton da ofishin sa ido kan yanar gizo na jami’ar Stanford ta kasar Amurka ya gabatar, inda ya ce, cikin shekaru da dama da suka gabata, kasar Amurka ta kafa tsarin fadakarwa mai girma ta kafafen sada zumunta game da kasashen Sin, da Rasha, da Iran da sauransu, don yada labarai marasa tushe da fadakar da harkokin siyasa ta hanyoyin bude shafunan jabu, da yada labarai kusan iri daya, domin jan hankalin mutane.

Kakakin ya kara da cewa, Amurka ce babbar mai yada labaran karya, amma tana ci gaba da daura laifi da bata sunan wasu kasashe. Ya ce a bayyane yake cewa, Amurka ta bude shafunan jabu da yawa, amma ta sa kaimi ga kafafen sada zumunta su rufe shafunan jama'ar Sin. Hakika Amurka ce mai yin tasiri kan ra’ayoyin jama’a, amma kuma ta mayar da dukkan kafofin watsa labaru na Sin a matsayin shafunan gwamnatin kasar. Kasar Amurka na shafawa kasar Sin bakin fenti, amma kuma sai take zargin kasar Sin din da yada ra’ayin kin Amurka. (Zainab)