logo

HAUSA

An Kammala Zaben Wakilan Da Za Su Halarci Babban Taron Wakilan JKS Karo Na 20

2022-09-25 20:46:14 CMG Hausa

An zabi jimilar wakilai 2,296 da za su halarci babban taron wakilan jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 20 dake karatowa.

Wata sanarwa da aka fitar yau, ta ce an zabi wakilan ne bisa kundin tsarin mulkin jam’iyyar, da tanade-tanaden kwamitin koli na jam’iyyar tare da aiwatar da dabarun da kwamitin ke bukata.

A cewar sanarwar, matsayin wakilan shi ne wakilci, bisa tanadin da kwamitin kolin JKS ya gindaya kan adadin wakilai daga bangarori daban daban. (Fa’iza Mustapha)