logo

HAUSA

Dalar Amurka, kaskar da ke shan jinin tattalin arzikin duniya

2022-09-25 19:51:21 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei

Domin neman dakile matsalar hauhawar farashin kayayyaki a gida, babban bankin kasar Amurka(FED) ya kara ruwan kudin ajiya da kaso 0.75% a kwanan baya, sau uku a jere ke nan da ya kara ruwan da wannan kaso a shekarar da muke ciki. Sakamakon matsayin dalar Amurka a tsarin harkokin hada-hadar kudi ta duniya, matakin da FED din ya dauka ya sa darajar dalar Amurka ta karu a kan sauran kudade, baya ga kuma farashin kayayyaki ya karu a duniya, matakin da kuma ya juya matsalar hauhawar farashin kaya da take fuskanta a gida zuwa sauran kasashe da shiyyoyi.

An ce, tun bayan karuwar darajar dalar Amurka a wannan shekara, darajar kudade 36 a sauran kasashen duniya ta ragu da a kalla kaso 1/10. Misali a nahiyar Afirka, darajar kudin Rand na kasar Afirka ta Kudu ta ragu da kashi 9.4%, yayin da darajar Pound na kasar Masar ta sauka da kashi 18%. A kasar Ghana ma, ko da yake ta riga ta daga ruwan kudin ajiya zuwa kashi 22% don tinkarar matakin kasar Amurka, duk da haka, darajar kudin kasar na ci gaba da raguwa. A Nijeriya da ta fi karfin tattalin arziki a Afirka, yawan hauhawar farashin kayayyaki ya kai kaso 19.64% a watan Yuli, baya ga kuma adadin ya hau kaso 20.52% a watan Agustan da ya wuce, wanda ya kai wani matsayin kolin tun bayan watan Satumban shekarar 2005. Abin da kuma ya biyo bayan matsalar hauhawar farashin kayayyaki shi ne dakushewar tattalin arziki, bisa rahoton hasashen tattalin arzikin Afirka na shekarar 2022 da bankin raya Afirka ya fitar a kwanan baya, an yi hasashen bunkasuwar tattalin arzikin Afirka da kaso 4.1% a wannan shekara, wanda ya fado kasa kwatankwacin kaso 6.9% da aka samu a shekarar 2021.

Ta hanyar saka matsalar hauhawar farashin kaya ga sauran kasashe, matsalar da Amurka din take fuskanta a cikin gida ta sassauta, duk da cewa hakan ya faru ne sakamakon hasarorin da sauran kasashe suke biya ta fannonin matsalar hauhawar farashin kaya da tabarbarewar tattalin arziki, lallai abin da mai iya magana kan ce, “Amurka ke ciwo, amma ta sa sauran kasashe su sha magani.”

A hakika dai, tun bayan karshen yakin duniya na biyu, Amurka ta sha yin amfani da kakkarfan matsayin dalar Amurka a duniya wajen kwatan arzikin sauran kasashe da ma saka matsalolinta gare su. Tamkar dai wata kaskar da ke jinin tattalin arzikin duniya ne, yadda Amurka ke amfani da dalarta wajen kwace dukiyoyin al’ummun sauran kasashe.

Hanya mafi kyau wajen daidaita wannan matsala ita ce, a rungumi manufar kiyaye kasancewar bangarori daban daban, wato kamata ya yi kasa da kasa, musamman ma kasashe masu tasowa su tsaya kan aiwatar da hadin gwiwa a tsakaninsu, wajen kafa wani tsarin hada-hadar kudi mai inganci da ke kunshe da kudade na kasashe daban daban. (Mai Zane:Mustapha Bulama)