logo

HAUSA

Kasashen tsibiran Pacific ba za su zamo makamin Amurka na aiwatar da siyasar yanki ba

2022-09-24 16:38:59 CMG Hausa

A ranar Alhamis, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ya jagoranci taron ministocin harkokin waje na kungiyar kawancen yankin Pacific ko PBP a takaice, a yayin babban taron MDD. Inda a lokacin ya yi ikirarin cewa, Amurka za ta himmatu sosai, ga bunkasa yankin tekun Pacifik, tare da hada kai tare da kasashen shiyyar wajen magance sauyin yanayi, da karfafa muhimman ababen more rayuwa da dai sauransu.

Kasashen waje sun yi imanin cewa, hakan tamkar share fage ne ga "Taron Amurka da Tsibiran Pacific" karo na farko, wanda za a gudanar a birnin Washington a karshen watan Satumbar nan.

A watan Yunin bana ne aka kafa kungiyar da ake kira PBP, kuma wasu kafofin yada labaran Amurka sun yi nuni da cewa, manufar PBP ita ce daidaita tasirin da kasar Sin ke da shi a yankin kudancin tekun Pacifik.

Bisa yanayin siyasar bangaranci ta Amurka, an yi watsi da kudancin Pacific cikin dogon lokaci, amma ko me ya sa a yanzu ake mayar da hankali a kan yankin? ‘Dan majalisar wakilan Amurka Steve Chabot, na da ra’ayin cewa, yarjejeniyar tsaron da aka kulla tsakanin Sin da tsibirin Solomon a farkon wannan shekara ta bukaci Amurka da ta aiwatar da matakai cikin gaggawa.

Muddin burin Amurka ba ya da tsarki, abu ne mai wuya kasashen tsibiran Pacific su amince da ita. Firayim ministan kasar Fiji Frank Bainimarama ya taba cewa, "Babban abin da ke damun mu, ba wai batun siyasar bangaranci ba ne, mun fi damuwa da batun sauyin yanayi."

A nasa bangare kuwa, wani jami'in bincike a cibiyar nazari ta Lowy dake kasar Australiya Mihai Sora, cewa ya yi "Shugabannin yankin tekun Pacific suna kyamar a yi amfani da su, a matsayin makamin aiwatar da siyasar yanki”.

A sa'i daya kuma, a ko da yaushe, Amurka tana kasancewa “Babban hadari mai saukar dan yayyafi” a fannin ba da agaji ga kasashen waje, lamarin da ya sanya kasashen dake tsibiran tekun Pacifik, ke nuna shakku kan alkawuran da ta dauka. (Mai fassara: Bilkisu)