logo

HAUSA

Kasashen Sin da Togo sun samu sakamako mai kyau a fannin hadin gwiwa

2022-09-24 17:06:09 CMG Hausa

A ranar 19 ga wata ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na Togo Faure Essozimna Gnassingbé, suka aikewa juna sakon taya murna, game da bikin cika shekaru 50 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu.

Game da hakan, jakadan kasar Sin a jamhuriyar Togo, Chao Weidong, ya bayyana a wata hira da ya yi da ‘yan jaridar kafar CMG a jiya Jumma’a cewa, tun bayan kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Togo, kasashen biyu sun nuna goyon baya ga juna, kuma sun samu manyan nasarori a fannin hadin gwiwa.

A fannin samar da ababen more rayuwa, bisa kwarya-kwaryar kididdiga, kasar Sin ta gina, ko gyara hanyoyin mota 17, da gadoji 12 a kasar Togo, wadanda ke saukaka zirga-zirgar jama'a, da jigilar kayayyaki. Kana wasu ayyuka, kamar babban filin jirgin saman kasa da kasa na Lomé, da hanyar Lomé da ta kewaye birnin, wadda bangaren Sin ya aiwatar, sun zama abun alfahari ga kasar Togo.

Baya ga haka, Chao Weidong ya ce, "Tun daga ranar 1 ga Satumbar nan, kasar Sin ta aiwatar da dage harajin sifiri, har kashi 98%, na kayayyakin dake fitowa daga Togo zuwa kasar Sin". (Mai fassara: Bilkisu Xin)