Yang Xiuyun mai shekaru 72 dake sha’awar wasan gudun dogon zango wato Marathon
2022-09-26 20:02:05 CRI
A kowace safiya, Yang Xiuyun mai shekaru 72 da haihuwa tana gudu a titin da ke gefen kogi, ta kuma shafe shekaru 22 da tana haka. Kafin ta yi ritaya, ba ta san mene ne gudun dogon zango ba. Amma, tun bayan da ta yi ritaya, ta yi gudun dogon zango kusan sau 40, har ma ta taba shiga gasar da aka shirya a Helsinki na kasar Finland. A cewarta, "Rayuwa kamar gudun dogon zango ce, ina gudu ne dai-dai da shekaru na”. To, masu sauraro, a cikin shirinmu na yau za mu kawo muku labari ne game da wannan baiwar Allah mai suna Yang Xiuyun.
Yang Xiuyun mai shekaru 72 da haihuwa, ta bayyana gudun kilomita 10 da safe a matsayin " abincin farko na yini".
Kafin ta yi ritaya, Yang Xiuyun ta kasance ma'aikaciyar kiwon dabbobi a wani yankin gonar da ke birnin Nanchang na lardin Jiangxi dake kudu maso gabashin kasar Sin, a lokacin, ba ta san mene ne gudun dogon zango ba ne, bayan da ta yi ritaya, ta yi irin wannan gudun kusan sau 40. Yang Xiuyun, wanda ta kwashe shekaru 22 tana gudun dogon zango, ta ce, "Rayuwa kamar gudun dogon zango ce, ina gudu ne dai-dai da shekaru na.”
A lokacin da ta yi ritaya ba da dadewa ba, Yang Xiuyun ta yi fama da ciwon koda, likita ya ce idan ba a yi mata tiyata ba, za ta iya samun sauki ta hanyar shan magani da motsa jiki. A lokacin, Yang Xiuyun ta kan ga mutane suna gudu a kan hanyar dake bakin kogi, ko mai ruwa ko mai iska suna wannan wasa.
Wata rana da safe, Yang Xiuyun ta fita yawo, sai ta sake saduwa da wannan rukunin masu gudu. Suna gudu tare, kuma kullum suna kara wa juna kwarin gwiwa. Ganin yadda Yang Xiuyun ta zuba musu idanu, sai masu tseren suka gayyace ta cikin farin ciki da ta shiga cikin tawagar tseren.
Da take waiwayen baya, Yang Xiuyun ta ce, "Da farko na ji tsoron zan rage saurin gudun su, amma sun karbe ni hannu bibbiyu."
Daga iya gudu na tsawon kilomita 5 zuwa kilomita 10, kilomita 20, har zuwa kilomita fiye da 42... Sannu a hankali Yang Xiuyun na kara iya gudu mai tsawo, a sa'i daya kuma, ta samu abokai masu sha’awar gudu wadanda ke zama kamar danginta.
A cikin tawagar masu gudun, wasu sun girme ta, amma yawancinsu ba su kai shekarunta ba, inda suke kiranta ‘yar uwa Yang. Yang Xiuyun ta ce cikin murmushi, yanzu muddin ba ta gansu na kwana daya ba, ba ta jin dadi a zuciyarta.
Gudu ya sauya jiki da tunanin Yang Xiuyun. A da, Yang Xiuyun kullum shiru take, amma yanzu gudu ya kara sanya ta cikin farin ciki da annashuwa.
A shekara ta 2006, Yang Xiuyun ta shiga kungiyar masu wasan gudun dogon zango ta Nanchang, kuma ta zama mambar rukunin farko na kungiyar.
A shekarar 2011, Yang Xiuyun ta rattaba hannu don shiga gasar gudun dogon zango ta Shanghai, ta kuma kammala gasar cikin sa’o’i biyar, amma duk da haka, ba ta gamsu da makin da ta samu a karon farko na gasar da ta shiga ba.
Tun daga wannan lokacin, ta nemi fayafayen bidiyo na koyar da dabarun gudu, inda ta koya tare da daidaita yadda ake gudu bisa mataki-mataki, kuma ta kan nemi wadanda suka kware a fannin gudu, don su koya mata wasu dabaru da suka shafi gudu yayin da ake motsa jiki da safe.
A shekarar 2012, Yang Xiuyun ta yi fama da ciwon jijiyoyi a kafarta ta dama, kuma ta daina gudu bayan da aka yi mata tiyata. Da dama daga cikin wadanda suke gudu tare da ita, sun yi tunanin cewa, Yang Xiuyun ba za ta sake yin gudu ba, amma bayan watanni 3 da yi mata tiyata, sai ta sake dawowa fagen gudu a hanyar dake bakin kogi da sanyin safiya, daga tafiya a hankali zuwa gudu, a cikin watanni 6 da take samun farfadowa, Yang Xiuyun ba ta taba daina gudu ba.
A shekarar 2016, Yang Xiuyun ta shiga gasar gudun dogon zango ta Hangzhou. Bayan shekaru biyar da samun horo irin na fasaha, ta kammala gudun a cikin sa'o'i 4 da mintuna 20, a yayin da take da shekaru 66 da haihuwa.
Yang Xiuyun ta ce, “Samun damar shiga tsaren, babbar nasara ce, bayan shafe shekaru da dama ina gudu, na fahimci cewa, ba za a kwatantawa gudun dogon zango da nake yi da na wasu ba.”
A shekarar 2019, Yang Xiuyun da abokanta masu sha’awar gudu sun rattaba hannu don shiga gasar gudun dogon zango ta Helsinki a kasar Finland.
Yang Xiuyun ta ce, "Bayan na kammala gudun, na ga cewa, 'yan kasashen waje da dama sun yaba min, ta hanyar daga yatsa a matsayina na tsohuwa. A wannan lokacin, na ji cewa ni na yi abin mamaki, wato mu tsoffi mata na kasar Sin ba rawa kawai muka iya ba.”
A wannan hutun yanayin zafi da ya gabata, karkashin jagorancin Yang Xiuyun, 'ya'yanta biyu da jikoki biyu su kan je bakin kogi don yin atisayen safe da karfe biyar ko shida na safe. Yang Xiuyun ta ce, yanzu ta kan yi gudun kilomita 10 cikin awa daya da rabi, gaskiya saurin gudun ya ragu fiye da da, amma a cewarta, ba za ta daina wannan wasan ba.