logo

HAUSA

An gudanar da taron kan yadda ake girmamawa da kare hakkin dan Adam a jihar Xinjiang ta kasar Sin.

2022-09-23 16:09:11 CMG HAUSA

 

Jiya ne, bisa agogon wuri, a yayin taro karo na 51 na kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD, tawagar din-din-din ta kasar Sin dake ofishin MDD a birnin Geneva da gwamnatin yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa suka gudanar da taron karawa juna sani, game da nasarorin da kasar Sin ta cimma wajen mutuntawa da kare hakkin dan-Adam a yankin Xinjiang.

Fiye da mutane 100 da suka hada da wakilan dindindin da manyan jami'an diflomasiyya daga kasashe fiye da 50 ne suka halarci taron.

Jakada Chen Xu dake zama zaunannen wakilin kasar Sin a ofishin MDD dake birnin Geneva, ya bayyana cewa, har kullum yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa na kasar Sin, yana nacewa wajen mayar da jama'a a gaban komai, da mutunta ra’ayin jama’a na samun rayuwa mai inganci. Don haka, ayyuka marasa dacewa da wasu kasashen yammacin duniya masu mugun nufi ke aikatawa, na neman bata sunan kasar Sin ba zai taba yin nasara ba. (Ibrahim Yaya)