logo

HAUSA

An yi gargadin samun ambaliyar ruwa a kudancin Nijeriya

2022-09-23 10:19:09 CMG HAUSA

 

Hukumar kula da agajin gaggawa ta Nijeriya NEMA, ta yi gargadi game da yiwuwar samun ambaliyar ruwa a jihohi 3 na kudancin kasar, yayin da aka yi hasashen samun ruwan sama mai karfi a kwanaki masu zuwa.

Shugaban hukumar NEMA a shiyyar kudancin kasar, Godwin Tepikor ne ya yi gargadin yayin wani taron manema labarai a birnin Fatakwal a jiya, inda ya yi kira ga gwamnatocin jihohin Rivers da Bayelsa da Cross-River, su kwashe mutanen dake zaune a wuraren dake fuskantar barazanar ambaliyar zuwa wurare masu tudu.

Ya kuma bukaci hukumomin agaji na jihohin su zauna cikin shirin ambaliyar da aka yi hasashe.

Darakta janar na hukumar Mustapha Habib Ahmed ya bayyana yayin wani taron kwararru a ranar Litinin cewa, kawo yanzu a bana, mutane a kalla 300 sun mutu sanadiyyar ambaliyar ruwa a wurare daban-daban na kasar, yayin da ake ci gaba da samun ruwan sama kamar da bakin kwarya. (Fa’iza Mustapha)