logo

HAUSA

An kusan kammala aikin gina babbar gada a Abidjan

2022-09-23 14:32:22 CMG HAUSA

 

A ran 22 ga wata, wani kamfanin kasar Sin ya kammala aikin hada gefuna biyu na wata babbar gada da aka gina ta a Bangko Bay na Abidjan, cibiyar tattalin arzikin kasar Cote d'Ivoire. Mashawarcin tattalin arziki da kasuwanci a ofishin jakadancin kasar Sin dake Cote d'Ivoire, Lu Jun ya halarci bikin murnar kammala aikin, har ma ya bayar da wani jawabi.

A cikin jawabi nasa, Lu Jun ya ce, an riga an sanya aikin a cikin shirin ci gaban kasar Cote d'Ivoire, ana fatan kamfanin Sin ya yi kokarin gaya tare da bangarorin Cote d’lvoire wajen kammala wannan muhimmin aiki, ta yadda za a iya kaddamar da shi da wurwuri. A sa’i daya kuma dole ne a tabbatar da inganci da tsaron aikin yadda ya kamata, a cewar Lu Jun. Ya kuma kara da cewa, ana fatan za a karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da Cote d’lvoire, ta yadda zumuncin al’ummun kasashen biyu da dangantakarsu za su shiga wani sabon mataki.

An fara aikin gina babbar gada mai tsawon kilomita 7.5 a Abidjan a ranar 31 ga watan Yulin shekarar 2018, wadda ta hada da wasu titunan birni da wasu kananan gadoji bakwai. Wannan aiki, wani muhimmin bangare ne na titunan birnin Abidjan, wanda zai kyautata yanayin zirga-zirgar birnin Abidjan da kuma ba da gudummawa wajen hada birnin da sauran yankunan Abidjan. (Safiyah Ma)