logo

HAUSA

Sojojin Najeriya sun hallaka 'yan ta'adda 36 a yankin arewa maso gabashin kasar

2022-09-23 09:54:16 CMG HAUSA

 

Mai magana da yawun rundunar sojojin Najeriya Musa Dan Madami, ya bayyana cewa, dakarunsu sun yi nasarar kashe a kalla ’yan ta’adda 36, a wasu hare-hare ta sama da sojojin suka kai a yankin arewa maso gabashin kasar cikin makonni biyu da suka gabata.

Musa Dan Madami ya shaidawa manema labarai a Abuja, fadar mulkin Najeriya, yayin wani taron manema labarai da aka shirya jiya Alhamis cewa, an kai harin ne da nufin fatattakar duk wasu tsagerun da ke addabar yankin arewa maso gabashin kasar.

Ya kara da cewa, kwamandoji biyu na kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi na Boko Haram, da na ISWAP na daga cikin wadanda aka kashe a tsakanin ranar 12 zuwa 15 ga watan Satumba, a lokacin da aka kai hare-hare ta sama a dajin Sambisa, dake zama babban maboyar 'yan ta'addan.

Jami’in ya ce, an yi nasarar kubutar da fararen hula 130 a yayin farmakin da sojojin suka kai. An kuma kama wasu mayakan Boko Haram 46, da wasu mutane 12 da ake zargin su na samar da kayan aiki ga mayakan. (Ibrahim)