logo

HAUSA

Ya kamata a tabbatar da hakkin dan Adam cikin rayuwar jama’a

2022-09-23 17:08:34 CMG Hausa

A kwanan baya, mukaddashiyar babbar kwamishina mai kula da hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya, Nada Al-Nashif ta bayyana a cikin wani jawabinta cewa, hauhawar farashin kayayyaki na haifar da barazana ga hakkin raya kai na jama’ar kasashe masu tasowa. A cewarta, yayin da asusun ba da lamunin duniya IMF ke hasashen ganin matsakaiciyar hauhawar farashin kayayyaki ta kashi 6.6% a kasashe masu sukuni a shekarar da muke ciki, hauhawar da ake sa ran ganinta a kasashe masu tasowa za ta iya kaiwa kashi 9.5%, bisa wani matsakaicin matsayi.

Batun nan bai ba ni mamaki ba, ganin yadda tun tuni kasar Amurka ke sanya bankunan kasar ba da karin ruwan kudin ajiya, don neman daidaita matsalar hauhawar farashin kaya a cikin gidanta. Sai dai matakin ya zama karkata matsin lamba da take fuskanta zuwa ga sauran kasashe, musamman ma kasashe marasa karfin tattalin arziki, wadanda suka fi jin radadin manufar. A sakamakon haka, zuwa yanzu, darajar kudin Rand na kasar Afirka ta Kudu ta ragu da kashi 9.4%, yayin da darajar Pound na kasar Masar ta sauka da kashi 18%. A kasar Ghana ma, ko da yake ta riga ta daga ruwan kudin ajiya zuwa kashi 22% don tinkarar matakin kasar Amurka, amma duk da haka, darajar kudin kasar na ci gaba da raguwa.

Kar mu manta da yadda kasar Amurka ke bayyana kanta a matsayin mai kare hakkin dan Adam a duniya. Amma ga shi yanzu tana kwatan moriya a kasashe marasa karfin tattalin arziki, tare da keta hakkin jama’ar kasashen na rayuwa da neman raya kansu. Ta wannan misali za mu iya ganin cewa, “kare hakkin dan Adam” da kasar Amurka take yi aikin fatar baki ne kawai, wanda sam ba zai haifar da moriya ga mutanen duniya ba.

Sai dai a nata bangare, yadda kasar Sin take fahimtar matakin “mai dokar barci ya buge da gyangyadi” da kasar Amurka ke dauka a fannin kare hakkin dan Adam, ya sa kasar ke kira ga kasashe daban daban don su dora karin muhimmanci kan kare hakkin dan Adam na raya kai da neman ci gaba. A gun taron kwamitin hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya dake gudana, wakilin Sin Chen Xu ya ce, ci gaban tattalin arziki shi ne tushen hakkin dan Adam. A cewarsa, ya kamata kasashe daban daban su yi kokarin tabbatar wa al’ummunsu hakki na gaske, kuma mai amfani.

Shin mene ne hakkin dan Adam na gaske kuma mai amfani?

Na tuna da wani saurayi mai aikin jigilar kaya da na gamu da shi a nan birnin Beijing a kwanan baya. Ya ce, ko da yake aikin da yake yi na kai abincin da aka saya ta yanar gizo ta Internet zuwa gidajen mutanen da suka sayi abincin na da wahala, amma yana samun Yuan 7 (kwatankwacin dalar Amurka 1) bisa duk wani kunshi da ya kai. Ya kan iya kai kunshi fiye da 100 a kowace rana, ta yadda yake samun fiye da Yuan 700 (fiye da dala 100) a duk rana. Hakan zai tabbatar da albashinsa na kowane wata da ya kai fiye da Yuan 15000 (dala 2122). To, wadannan adadi su ne shaidar hakkin dan Adam na gaske.

Ban da wannan kuma na tuna da wani kauye mai suna “Xiao Hei Fa” da na kai ziyara a kwanan baya, inda na ga gwamnati na ba da tallafi ga wasu kamfanoni, domin su samar da guraben aikin yi ga mutane masu fama da lalurar nakasa. Ta wannan hanya wadannan nakasassu sun samu kudin shigar da ya kai fiye da Yuan dubu 25 (dalar Amurka 3540) a duk shekara, abun da ya sa suke iya dokaro da kansu. Wannan irin manufar taimakawa nakasassu ita ce abin da ake kira manufar kare hakkin dan Adam mai amfani.

Hakkin dan Adam bai tsaya ga kalmomi kawai ba, ya kamata a yi kokarin tabbatar da shi a cikin rayuwar jama’a. Ta hanyar tantance yanayin rayuwar jama’a, za a san ainihin yanayin hakkin dan Adam na wata kasa. (Bello Wang)