logo

HAUSA

Wang Yi ya halarci taron ministoci harkokin waje na Kwamitin Sulhu MDD

2022-09-23 14:43:19 CMG HAUSA

 

Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya halarci taron ministocin harkokin waje na kwamitin sulhu na MDD game da batun Ukraine, jiya a hedkwatar majalisar dake birnin New York.

Wang Yi ya ce matsayin kasar Sin dangane da batun Ukraine a bayyane yake kuma bai sauya ba. Yana mai cewa ya kamata a goyi bayan girmama cikakken iko da yankunan dukkan kasashe, da kiyaye ka’idoji da manufofin MDD, da batutuwan tsaro dake ciwa dukkan bangarori tuwo a kwarya, da kuma dukkan kokarin warware rikicin cikin lumana.

Ya ce matsayin da kasar Sin ta dauka game da yanayin da ake ciki yanzu, sun hada da na farko, a nace ga tattaunawa da yarjejeniyoyi. Na biyu, a hada hannu domin kare yanayin daga ta’azzara. Na uku, wajibi ne a kula da ayyukan agaji, kana na hudu, a yi dukkan mai yiyuwa wajen ganin rikicin bai fadada ba. (Fa’iza Mustapha)