logo

HAUSA

Moriyar gasar Olympic da kasar Sin ta gudanar na kayatar da duniya

2022-09-22 13:46:55 CRI

Bikin baje kolin cinikayyar hidimomi na kasa da kasa na shekarar 2022, wanda aka gudanar a birnin Beijing na kasar Sin ko CIFTIS a takaice, ya haifar da babbar moriya a fannin raya sha’anin wasanni, har ma kwararru da dama na cewa, ribar da aka samu a wannan fanni, ta hada da wanzar da bunkasar wasannin kankara, da masana’antun dake da nasaba da hakan.

A cewar shugaban kwamitin shirya gasar Olympic na kasa da kasa Thomas Bach, birnin Beijing ya yi rawar gani, wajen shirya kasaitacciyar gasa a shekarar nan ta 2022, wanda hakan ya bude wani sabon babi na raya wasannin kankara da dusar kankara, tare da shigar da al’ummar kasar Sin sama da miliyan 300 cikin harkokin wasan kankara.

Cin cikakkiyar gajiya daga gasar Olympic

Gundumar Yanqing, na daya daga wuraren da suka karbi bakuncin wasannin Olympic na shekarar 2022 da birnin Beijing ya karbi bakunci, kuma a cewar mataimakin shugaban gundumar Yanqing Ren Jianghao, fatan su shi ne dorewar gajiyar da gasar Olympics ta lokacin hunturu ta samar. Ren Jianghao ya ce wajibi ne a tabbatar da dorewar nasarar da aka cimma a yayin gasar ta Olympics.

A cewar sa, "Akwai hanyoyi 3 na cimma wannan buri. Na farko, mun samu kwarewa ta fuskar gudanar da gasar Olympics ta lokacin hunturu, don haka mun gabatar da karin gasanni masu inganci a Yanqing. Na biyu, mun gabatar da shawarar gina tsarin da zai mayar da Yanqing wani yanki na harkokin wasanni, ba wai wasannin lokacin hunturu kadai ba. Na uku, muna da lambun masana’antun wasanni a Yanqing, wanda ke jawo tarin kamfanonin fasahar wasanni hunturu. Kaza lika karamar hukuma ta fitar da manufofi na cimma wadannan burika".

Tun bayan da birnin Beijing ya cimma nasarar zama mai masaukin bakin gasar Olympics ta lokacin hunturu, aka kuma amince ya karbi bakuncin gasar tare da birnin Zhangjiakou, wuraren sun ci gaba da samun sauye sauye, inda suka mayar da wuraren ginshikan bunkasa tattalin arziki mai nasaba da wasannin kankara.

Sakamakon haka, an gina wuraren zamiyar kankara 9 a Zhangjiakou, da wuraren itisaye 59, da makarantun horaswa 100, an kuma gudanar da manyan gasanni sama da 100, da suka hada da Freestyle Skiing, da Snowboarding, da Slopestyle Chase na matakin kasa da kasa. Baya ga haka, an kaddamar da ayyukan da suka shafi masana’antun wasannin hunturu har 115, ciki har da na kamfanin France MND. Kaza lika bayan gudanar da gasar ta Olympics ta lokacin hunturu, manyan wuraren gudanar da wasannin kankara, da tsarin gudanarwa, da tawagogin shirye shirye, da fannin samar da kayan da suka jibanci wasannin na lokacin hunturu, duk sun zama riba.

Mataimakin magajin garin Zhangjiakou Liu Haifeng, ya bayyana cewa, "Za mu yi aiki tukuru wajen tabbatar da an yi amfani da wuraren wasannin, da dukkanin kayayyakin dake cikin su da kyau, ta yadda za a ci gajiyar su bayan wucewar gasar ta Olympic. Za mu aiwatar da tsarin da aka yi na wanzar da cin gajiya daga gasar Olympics ta lokacin hunturu, tare da ci gaba da gudanar da gasannin kasa da kasa da na cikin gida a wuraren".

Daga matsayin masana’antar shirya wasannin kankara

Mene ne muhimmancin daga matsayin masana’antar shirya wasannin kankara ta Sin?

A cewar daraktan gamayyar kungiyar ‘yan wasan kankara ta kasar Sin Zheng Liangcheng "Gasar Olympic ta lokacin hunturu da birnin Beijing ya karbi bakunci, ta haifar da kafuwar yankunan gudanar da wasannin kankara da na dusar kankara, wanda hakan ya samar da damar fadada fannin masana’antun wasannin lokacin hunturu. Zheng ya ce yanzu haka kasar Sin na da wuraren wasannin kankara 803, sai dai hakan na tattare da kalubale. Ya ce hanya mafi dacewa ta kawar da matsaloli a fannin ita ce daga matsayin wuraren gudanar da wasannin.

Zheng ya kara da cewa "Asalin masana’antar wasannin hunturu, ta samar da damar fadada ababen more rayuwa a fannin wasanni, amma idan ba a samu karin bukatar masu shiga wasannin a cikin ‘yan shekaru masu zuwa ba, abubuwan da masana’antar ke samarwa za su wuce bukatar masu amfani da su, wanda hakan zai haifar da kalubale”.

Masana a wannan fanni na ganin daga matsayin fannin, yana da alaka da yanayin wurare, da kasancewar wuri na sarrafa hajojin wasan ko kuma na cinikayyar su, da ma batun kimiyya da fasaha.

Zheng Ya ce “A yayin gasar Olympics ta lokacin hunturu da birnin Beijing ya karbi bakunci, Sin ta zuba jari mai tarin yawa a fannin binciken kimiyya, wanda hakan ya haifar da manyan nasarori. Idan muka aiwatar da hakan a sassa masu zaman kan su, sashen masana’antu masu nasaba da fannin su ma za su inganta”.

A yayin baje kolin cinikayyar ba da hidima ko CIFTIS, wanda ya gabata a kwanan nan, da yawa daga mahalarta baje kolin sun nuna sabbin fasahohi, da kayayyaki masu alaka da wasannin kankara. Kaza lika wasu kwararru na ganin wasu daga filaye ko wuraren da aka gudanar da wasannin kankara, za su iya zama wuri da zai taimakawa kare muhalli da ruwa, da lantarki, da kyautata ayyuka masu nasaba da hakan; Irin wadannan wurare da kayan aiki da aka tanada, da masaukan baki, za su kara inganta kwarewar ‘yan kasa game da harkokin wasannin hunturu, da hidimomi masu alaka da hakan. Don haka ya dace a wanzar da ci gaban fannin yadda ya kamata.

Taron baje koli na CIFTIS, ya hallara kasashe da yankuna sama da 30, kuma sashen sa na nune nunen hidimomin wasanni, ya bude wata kafa ga duniya ta raya wasanni a lambun shakatawa na Shougang.

Game da hakan, mataimakin magajin garin birnin Zhangjiakou Liu Haifeng, ya bayyana cewa, a nan gaba, za a karfafa musaya da hadin gwiwa tsakanin biranen gasar Olympic ta lokacin hunturu, da sauran birane da hukumomin kasa da kasa, kana za a kafa kamfanin musamman na samar da kayayyakin da ake bukata, tare da kafa wata cibiya ta kasa, wadda za ta rika samar da daukacin kayayyakin wasannin da ake da buakata.

Jami’in ba da shawara game da kiwon lafiya da jin dadin jama’a, da wasanni a ofishin jakadancin Netherlands dake kasar Sin Shi Mingkang, ya yi tsokaci kan wannan mataki, yana mai cewa “Netherlands za ta yi aiki tukuru, wajen bunkasa musaya da Sin a fannin raya wasannin hunturu. Muna fatan zurfafa hadin gwiwa da Sin. Wasu daga kamfanonin Netherlands suna zuba jari a biranen Shanghai da Beijing. Ina ganin hakan hanya ce mai dacewa ta yin aiki, domin karfafa gwiwar matasa su kara shiga wasannin kankara, ba kawai a birane ba, har ma da kauyuka da garuruwa. Karfafa musaya tsakanin sassan kasa da kasa na da muhimmanci sosai wajen cimma nasarar gudanar da sauye sauye, a bangaren samar da kayayyakin da ake bukata domin wasannin hunturu, da kuma kafa sabuwar kasuwa a fannin.