logo

HAUSA

Sin Ta Mayar Da Martani Game Da Zargin Da Amurka Da Birtaniya Suka Yi Mata Kan Hakkin Kananan Kabilu

2022-09-22 16:23:31 CMG HAUSA

Zaunannen wakilin Sin dake MDD Zhang Jun ya gabatar da jawabi a babban taron manyan shugabanni na tunawa da cika shekaru 30 da zartas da sanarwar hakkin kananan kabilu ta MDD, inda ya mai da martani ga zargin da wasu kasashen yamma ciki hadda Amurka da Birtaniya da wakilan EU suka yi mata kan hakkin kananan kabilu.

Zhang Jun ya ce, yanzu kabilar Han da Uygur da Kazakh da sauran kabilu 56 suna rayuwa cikin jituwa a yankin Xinjiang, ana samun bunkasuwar tattalin arzikin mai dorewa da kyautatuwar al’umma da ci gaban al’adu da kuma bin addinai yadda ya kamata a yankin, bisa gudunmawar da kowa ya bayar, lamarin da ba za a iya musanta ba ko kadan.

Amma, abin takaici shi ne, wakilan wasu 'yan kasashe irin su Amurka da Birtaniya da Tarayyar Turai, sun yi fatali da gaskiyar lamarin tare da cin zarafin babban taron MDD da ma taron na yau, inda suka zargi kasar Sin da cin zarafi marasa tushe, lamarin da kasar Sin ke nuna adawa da shi matuka

Zhang ya kara da cewa, Sin ta yi kira ga kwamiti mai kula da hakkin Bil Adama da jami’in musamman mai kula da harkokin kananan kabilu, da su ci gaba da mayar da hankali kan laifufukan da Amurka da sauran kasashe suke aikatawa game da keta hakkin kananan kabilu. Kasar Sin ta kalubalanci wasu kasashe, da su daina siyasantar da batutuwan da suka shafi hakkin Bil Adama da dakatar da nuna fuska biyu, da daina tsoma baki a harkokin cikin gidan sauran kasashe, a maimakon hakan, su mai da hankali kan bukatun jama’arsu don kyautata yanayin hakkin dan Adam a kasashensu. (Amina Xu)