logo

HAUSA

Sin ta samu ci gaba a ginin tashar sadarwa ta 5G

2022-09-22 10:47:19 CMG Hausa

Ma’aikatar kula da masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin, ta ce adadin tashoshin samar da tsarin sadarwa na 5G dake kasar Sin na karuwa, yayin da kasar ke kokarin inganta ginin tsarin sadarwar a shekarun baya bayan nan.

Alkaluma daga ma’aikatar sun nuna cewa, zuwa karshen watan Agusta, kasar Sin na da tashoshin 5G sama da miliyan 2.1, wanda ya dauki kaso 19.8 na tashoshin samar da 5G din ga na’urorin tafi da gidanka, adadin da ya karu da kaso 5.5 daga karshen shekarar 2021.

Haka kuma, cikin watanni 8 na farkon bana, an gina karin tashoshin 5G 677,000 a kasar.

Har ila yau, ma’aikatar ta ce adadin masu amfani da 5G a na’urorin tafi da gidanka a kasar Sin, ya kai miliyan 475 a karshen watan Yuli.

Rahoton hukumar kididdiga ta kasar Sin ya ruwaito cewa, kasar ta gina tsarin sadarwar 5G mafi girma a duniya. Kuma zuwa karshen shekarar 2021, adadin tashoshin 5G a kasar ya dauki sama da kaso 60 na duniya baki daya. (Fa’iza Mustapha)