logo

HAUSA

Shugaba Xi ya mika sakon taya murna gabanin bikin girbin amfanin gona na manoman kasar Sin

2022-09-22 20:42:53 CMG Hausa

Babban sakataren kwamitin kolin JKS kuma shugaban kasar Xi Jinping, ya mika sakon taya murna a madadin kwamitin kolin JKS, ga daukacin manoman kasar, da sauran wadanda ke gudanar da ayyuka daban daban masu nasaba da noma da raya karkara, gabanin bikin girbin amfanin gona na manoman kasar Sin karo na 5.

Xi, ya kuma jaddada muhimmancin tabbatar da ci gaba wajen farfado da kauyuka, da aiwatar da matakan samar da wadata, da jin dadin rayuwa, da kyakkyawan muhalli ga mazauna yankunan karkara.   (Saminu Alhassan)