logo

HAUSA

Wakilin Sin ya yi kira da inganta ayyukan raya duniya da kare ’yancin kowa

2022-09-22 11:23:19 CMG Hausa

Wakilin Sin a ofishin MDD dake birnin Geneva da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake kasar Switzerland, Chen Xu, ya halarci taron kwamitin kare hakkin dan Adam karo na 51 tare da yin jawabi, inda ya yi kira ga kasashen duniya, da su bunkasa shawarar ci gaban duniya, da tabbatar da kare muhimman hakkokin dan Adam da doka ta baiwa mutane, da karfafa hadin gwiwar kasa da kasa, don ganin an aiwatar da ajandar 2030, da gina al’umma mai makoma bai daya ga daukacin bil-adama.

Chen Xu ya jaddada cewa, ci gaba shi ne tushen hakkin dan Adam. Shawarar ci gaban kasa da kasa da shugaban Xi Jinping ya gabatar, yana daya daga cikin kayayyakin more rayuwa da gudummawa da Sin ta samar wa duk duniya wajen inganta hakkin dan Adam na duniya.

Al’ummar kasa da kasa ta ba da amsa mai kyau, kuma fiye da kasashe 100 sun nuna goyon baya ga wannan batu. Bangaren Sin yana fatan sanya aikin neman bunkasuwa a matsayin nauyi mai muhimmanci dake bisa wuyan dukkan kasashen duniya, ta yadda za a iya ci gaba da aiwatar da shawarar akai-akai, da farfado da hadin gwiwar kasa da kasa game da aiwatar da ajandar shekarar 2030, da inganta cimma burin samun ci gaba a fadin duniya, da gina makoma mai kyakkyawar makomar bai daya ga dukkan bil-Adam. (Safiyah Ma)