logo

HAUSA

Kwararru na Sin da Afrika sun bukaci a rungumi tsarin samar da abinci mai kare halittu

2022-09-22 10:08:23 CMG Hausa

Masana daga Sin da Afrika, sun bayyana fadada amfani da tsarin samar da abinci ta hanyar kare halittu a matsayin jigon magance matsaloli 3 dake barazana ga jituwa tsakanin halittu da dan adam, da suka hada da sauyin yanayi da asarar hallitu da muhallansu da gurbatar yanayi.

Masanan da suka bayyana haka yayin wani taro ta kafar bidiyo, sun kara da cewa, sauya tsarin aikin gona daga amfani da sinadarai zuwa mai kare halittu, ka iya magance asara da gurbatar muhallin halittu da matsalolin yanayi dake addabar kasashe masu tasowa.

Zhu Chunquan, shugaban shirye-shiryen kasar Sin na kare halittu a babban taron tattalin arziki na duniya, ya ce jituwa tsakanin sauran hallitu da dan adam na iya dorewa da zarar tsarin samar da abinci ya yi daidai da inganta kare halittu da muhallansu, kamar dazuka da yankunan ruwa.

A nasa bangare, mai bincike da rajin kare muhalli a cibiyar kula da mabanbantan halittu ta Afrika ACB, Linzi Lewis, cewa ya yi, ya kamata a daidaita tsarin samarwa da adanawa da rarrabawa da amfani da kayayyakin gona, da dabarun amfani da makamashi mai tsafta, domin rage fitar da hayaki mai gurba da gurbatar muhalli.

Shi kuma Jiang Gaoming, mai bincike a cibiyar nazarin tsirrai ta cibiyar kimiyya ta kasar Sin, ya jaddada cewa, karfafawa manoman gwiwa, zai taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsarin samar da abinci, ya dace da kare halittu, kana ya zama mai juriya ga matsalar yanayi dake ta’azzara. (Fa’iza Mustapha)