logo

HAUSA

Duniya na matukar bukatar hadin kai sama da ko wane lokaci a tarihi

2022-09-22 20:15:00 CMG Hausa

Sanin kowa ne cewa, a yanzu haka duniyar bil adama na fuskantar manyan kalubale, da matsaloli a matakai daban daban, wasu na kasa da kasa, wasu kuma na shiyyoyi.

Matsalolin ci gaba da yaduwar annobar COVID-19, da rikicin Ukraine, da kamfar cimaka, da yaduwar fatara, da kalubalen sauyin yanayi, kadan ne daga cikinsu. Hakan ne ma ya sa a cikin jabawin da ya gabatar yayin bude babban taron MDD na 77, babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya tabo batun bukatar da ake da ita, ta hada karfi da karfe wajen shawo kan matsalolin duniya.

Mr. Guterres ya nuna damuwa, game da yadda duniya ke kara fuskantar baraka, da watsi da tattaunawa, ko aiwatar da matakan warware matsaloli cikin hadin gwiwa. Har ma yake cewa, a baya bayan nan, duniya na tunkarar yanayi na rashin hadin gwiwa kwata-kwata, daga dan hadin kai kalilan da a baya ake da shi.

Ko shakka babu wannan batu haka yake, duba da yadda ake ta samun rarrabuwar kawuna masu haifar da tashe-tashen hankula, a sassa daban daban na duniya. Wasu sassa suna kafa kawance domin muzgunawa wasu, suna watsi da dokokin kasa da kasa, wanda hakan tamkar yin watsi da dimokaradiyya ne, da ma sauran matakai na inganta hadin gwiwar kasa da kasa.

A lokutan da suka shude da ma a yanzu, tarihi ya nuna bukatar da dan Adam ke da ita ta hada kai da juna, a matsayin hanya daya tilo ta wanzar da ci gaba. Don haka a yanzu ma, lokaci ne da ya kamata shugabannin duniya su rungumi hadin kai, da “hada karfi da karfi” wajen shawo kan kalubalen dake addabar duniya baki daya.

Masana dai sun sha bayyana cewa, ba wani bangare, ko kasa mai karfi daya tilo, wadda za ta ita warware matsalolin ta, ko wadanda suke addabar duniya baki daya ita kadai. Hakan na nufin idan har ana son kaiwa ga warware kalubalen da duniya ke ciki a yanzu da ma nan gaba, ya zama dole a komawa hadin gwiwa da zaman jituwa. (Saminu Hassan)