Dole ne Japan ta fuskanci ra'ayin jama'a don dakatar da zubar da ruwan dagwalon nukiliya cikin teku
2022-09-22 22:03:50 CMG Hausa
Jiya Laraba, wasu kungiyoyi masu zaman kansu na kasar Japan, sun gabatar da takardar da kimanin mutane 42,000 suka sanyawa hannu cikin hadin gwiwa ga Kamfanin Lantarki na Tokyo, da Ma'aikatar Tattalin Arziki da Masana'antu ta Japan, inda suke adawa da shirin zubar da ruwan dagwalon nukiliyar tashar makamashin nukiliya ta Fukushima Daiichi cikin teku, da kuma neman gwamnatin Japan da ta dauki wasu matakan magance hakan. A cewar kamfanin dillancin labaru na Kyodo News, tun daga watan Yunin bara, an tattara jimillar sa hannun 221,000 a duk fadin Japan.
Sakamakon karuwar ruwan dagwalon Nukiliya, gwamnatin Japan ta yi ikirarin cewa, tekun na da karfin da ake kira wai "tsarkake kansa", kuma ta kara kaimi wajen fitar da ruwan dagwalon a cikin tekun, da nufin yin amfani da wannan hanya mafi arha ta fuskar tattalin arziki don warware matsalar.
Kididdigar da cibiyar binciken kimiyyar ruwa ta Jamus ta fitar, ta nuna cewa, daga ranar da aka zubar da dagwalon, zuwa kwanaki 57 kacal gurbataccen ruwan zai iya bazuwa zuwa yawancin yankin Tekun Pasifik, kuma a cikin shekaru 3 kacal, ruwan dagwalon nukiliyar zai watsu zuwa yankunan da suka shafi Amurka, da Canada da Austiraliya.
Yadda za a tinkari matsalar ruwan dagwalon nukiliyar tashar makamashin nukiliya ta Fukushima Daiichi, na da alaka da tsaron yanayin muhallin ruwa na duniya, da kiwon lafiyar jama’ar duk kasashe. Don haka bai dace a saba wa ra’ayin jama’a ba. Duba da adawar da ‘yan kasar Japan suke yi cikin hadin gwiwa, ko kuma adawa mai karfi daga jama’ar kasashen da ke makwabtaka da ita, dole ne gwamnatin kasar Japan ta tinkari, tare da ba da amsa, sannan ta dakatar da shirin ta mai hatsarin gaske, na zubar da ruwan dagwalon nukiliya cikin teku. (Mai fassara: Bilkisu Xin)