logo

HAUSA

Masana: Tattalin arzikin Afirka na fuskantar barazanar sauyin yanayi da rashin tsari

2022-09-21 11:20:48 CMG HAUSA

 

Masana sun bayyana cewa, matsalar sauyin yanayi, da rashin tabbas a fannin siyasa da ka'idoji, na haifar da barazana ga dorewar ci gaban tattalin arziki a nahiyar Afirka.

A jawaban da suka gabata a yayin kaddamar da rahoton shekarar 2022 dangane da alkaluman sakamakon hadurran dake shafar tattalin arzikin nahiyar, kwararrun sun bayyana cewa, ya kamata nahiyar ta fuskanci barazanar rikice-rikice dake faruwa loto-loto, da matsalar sauyin yanayi, da rashin tabbas a bangaren manufofi da tsare-tsare, don samun dorewar ci gaban tattalin arzikin.

Babbar mai nazari dake kula da yammacin Afirka, a wani kamfani mai ba da shawara kan dabarun tunkarar kasadar kasa da kasa, Patricia Rodrigues ta yi nuni da cewa, yunkurin Afirka na farfado da tattalin arziki yana cikin hadari, sakamakon barkewar annobar COVID-19, da rikicin Ukraine da Rasha da kuma matsalar fari da ke faruwa.

Ta kara da cewa, sauye-sauyen siyasa,da karuwar basussukan gwamnatoci da gibin ababen more rayuwa, sun kara dakile saka hannun jarin kasashen waje kai tsaye a nahiyar, lamarin da ya shafi ga ci gaban tattalin arzikin nahiyar.

Darektan kula da harkokin dake yiwa tattalin arziki barazana na nahiyar Afirka Vincent Rouget ya ce, kamata ya yi nahiyar ta yi amfani da ingantattun manufofi da tsarin mulki, da kirkire-kirkire, da hadewa da tsarin samar da kayayyaki na duniya, domin kara karfin tattalin arzikin nahiyar, a gabar da ake fuskantar tashe-tashen hankula da sauyin yanayi a sassan duniya.

Rouget ya ce, amfani da damar da yankin ciniki cikin 'yanci na nahiyar Afirka (AfCFTA) ya samar, da inganta masana'antu na cikin gida, zai iya haifar da ci gaban sabbin masana’antu na cikin gida dake samar da dimbin guraben ayyukan yi ga matasa.

Zainab Animashaun, babbar mai nazarci a kan dabarun kare hadurra dake shafar tattalin arziki, ta ce kamata ya yi gwamnatocin Afirka su yi amfani da kyawawan manufofi da tsare-tsare, a wani yunkuri na tinkarar matsalar hauhawar farashin kayayyaki da ke haifar da nakasu ga ci gaban nahiyar cikin dogon lokaci. (Ibrahim Yaya)