Yadda mahukuntan kasar Sin suka yi kokarin daukar matakan tabbatar da ikon kiwon lafiyar fararen hula
2022-09-21 09:42:40 CMG Hausa
Har kullum dan Adama na fatan gudanar da kyakkyawar rayuwa, tun daga yarinta har zuwa tsufa. Har ma masana da dama na danganta tsawon rayuwar al’ummun kasashe daban daban, da nasarar cikar wannan muhimmin buri.
Masana da dama na ganin cewa, tsawon rai na al’ummun wata kasa, daya ne daga cikin muhimmin mizani dake tabbatar da nasarar wannan kasa a fannin ci gaba. Kuma a zahiri, kasashe masu ci gaba, al’ummunsu suna fin na sauran kasashe matalauta tsawon rayuwa. Babban dalili game da hakan shi ne, yadda al’ummun kasashe masu ci gaba ke samun kyakkyawan tsarin kiwon lafiya, da isasshen abinci mai gina jiki, da tsaro, da tattalin arziki mai yalwa. Hakan na taka rawa kwarai ga tsawon rayuwar bil adama.
A baya bayan nan, wasu alkaluma sun nuna yadda al’ummun kasar Sin ke samun karin tsawon rai, inda sabbin alkaluma da mahukuntan kasar suka fitar suka nuna cewa, matsakaicin tsawon ran al’ummar kasar a yanzu, ya karu daga shekaru 76.79 a shekarar 2019, da shekaru 76.96 a shekarar 2020, zuwa shekaru 78.2 a shekarar 2021 da ta gabata. Wannan adadi a cewar alkaluman kididdiga, ya haura na al’ummar Amurka, wadanda nasu matsakaicin tsawon ran ya yi kasa a shekarar 2021 zuwa shekaru 76.1.
Babban darasi game da ci gaban da kasar Sin ta samu a wannan fanni shi ne, jajircewar hukumomin kasar, karkashin jagorancin JKS, wajen tsara manufofi daban daban, na inganta kiwon lafiya, da kandagarkin cututtuka, da samar da abinci isasshe, da yaki da fatara, da manufofin musamman na kula da rayuwar tsofaffi. Baya ga muhimmin mataki na habaka cin gajiya daga ilmomin kimiyya da fasaha, wadanda ke taka muhimmiyar rawa wajen kyautata rayuwar dan Adam. (Ibrahim Yaya, Saminu Hassan, Sanusi Chen)