logo

HAUSA

MDD: Mummunan fari ya raba sama da mutane miliyan 1.1 da gidajensu a Somaliya

2022-09-21 11:19:59 CMG HAUSA

 

Hukumar kula da ayyukan jin kai ta MDD (OCHA) ta bayyana cewa, adadin mutanen da suka rasa matsugunansu a Somaliya sakamakon fari, ya karu zuwa sama da miliyan 1.1, tsakanin watan Janairun shekarar 2021 zuwa watan Agustan shekarar 2022.

Ofishin OCHA ya ce, kimanin mutane 98,900 ne fari ya rutsa da su a cikin watan Agusta, adadin da ya karu da kashi 18 cikin 100, idan aka kwatanta da watan da ya gabata.

Alkaluman baya-bayan nan na zuwa ne, a daidai lokacin da abokan hadin gwiwa suka fadada ayyukansu na tunkarar fari cikin gaggawa, inda suka kaiwa mutane miliyan 5.3 agaji da kariya a watan Agusta, sama da mutane miliyan 3.4 da aka taimakawa a watan Yuni.

A cewar OCHA, hukumomin ba da agaji, sun fi ba da fifiko ga wuraren da ke da matukar bukata, tare da karfafa hadin gwiwa a gundumomi 38 da kuma kai kayan agajin gaggawa ga wadanda suka fi tsananin bukata, daga cikin sabbin mutanen da suka rasa matsugunansu.

Ayyukan MDD na cewa, za a yi fama da yunwa a sassan kasar a tsakanin watannin Oktoba zuwa Disamba, muddin ba a hanzarta kai agajin ceton rai ga mutanen da suka fi bukata ba. (Ibrahim)