logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi kira da a dakatar da bude wuta

2022-09-21 21:32:58 CMG Hausa

Kasar Sin ta yi kira da a dakatar da bude wuta, ta hanyar gudanar da shawarwari da tuntuba, a gabar da shugaban Rasha Vladimir Putin ya gabatar da jawabi dangane da batun kasar Ukraine, inda ya ce ya amince da shigar da karin dakaru 30,000 dake jiran ko ta kwana.

Da yake tsokaci game da batun, a yayin taron manema labarai na Larabar nan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya yi kira da a gaggauta kaiwa ga lalubo bakin zaren warware kalubalen tsaro, da dukkanin sassan da batun ya shafa ke nuna damuwa a kai.

A karon farko tun bayan yakin duniya na biyu, shugaba Vladimir Putin ya sanya hannu kan umarnin shugaba, wanda ya tanadi tura dakarun dake jiran ko ta kwana, zuwa fagen daga a Ukraine.  (Saminu Alhassan)