logo

HAUSA

Bikin baje koli na CIIE: Manema labaru za su iya rajista yanzu

2022-09-21 11:05:35 CMG Hausa

Ana shirin gudanar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su cikin kasuwannin kasar Sin daga ketare na CIIE karo na 5, a birnin Shanghai dake gabashin kasar, tsakanin ranar 5 zuwa 10 ga watan Nuwamban dake tafe. Bayanai na cewa, manema labaru dake da sha’awar halartar bikin, za su iya yin rajista daga yau 21 ga watan Satumba, har zuwa ranar 10 ga watan Oktoba mai zuwa.

Manema labaru za su iya yin rajista ta shafin yanar gizo ta Internet ta bikin baje kolin CIIE, wato www.ciie.org, da kuma manhajar APP din musamman ta bikin CIIE.

Rahotanni na cewa, galibin maneman labaru da za a gayyata su ne na kafofin watsa labaru cikin gidan kasar, ko kuma ‘yan jarida na kasashen waje da suke cikin kasar Sin, don tabbatar da kandagarkin yaduwar cutar COVID-19. (Bello Wang)