logo

HAUSA

Wang Yi ya shugabanci taron ministoci na kasashe masu rungumar shawarar samar da ci gaban duniya

2022-09-21 21:18:02 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya shugabanci taron ministoci na kungiyar kasashe masu rungumar shawarar samar da ci gaban duniya (GDI).

Wang Yi, ya jagoranci taron na GDI ne a jiya Talata, a gefen babban taron MDD dake gudana a birnin New York. Yayin zaman, minista Wang ya bayyana matakan da mambobin zaman za su dauka na ingiza tallafawa ayyukan dake kunshe cikin ajandar MDD ta wanzar da ci gaba nan da shekarar 2030.

A watan Janairun bana ne aka kaddamar da kungiyar kasashe masu rungumar shawarar samar da ci gaban duniya a hedkwatar MDD dake New York, kuma kawo yanzu, sama da kasashe 60 sun shiga kungiyar.
Da yake karin haske game da batun, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yayin taron manema labarai na Larabar nan cewa, shawarar ta GDI na mutunta akidar yin komai a bude, da tafiya tare da kowa. Wang ya yi maraba da abokan aiki na kasashe masu wadata, da su shiga a dama da su a ayyukan hadin gwiwa da tallafi, su yi aiki tare, wajen daga matsayin ci gaban duniya zuwa mataki na gaba, ta yadda za a kai ga hada karfi da karfe don cimma nasarorin bunkasa ci gaban duniya mai dorewa kamar yadda aka tsara.  (Saminu Alhassan)