logo

HAUSA

Wang Yi ya halarci dandalin tattaunawa kan harkokin tsaro na yankin Gabas ta Tsakiya

2022-09-21 21:02:11 CMG Hausa

Memban majalisar gudanarwa ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya halarci bikin kaddamar da dandalin tattaunawa kan harkokin tsaron yankin Gabas ta Tsakiya karo na biyu, ta kafar bidiyio a yau Laraba.

Wang ya jaddada cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fitar da shawarar tsaron duk duniya a watan Afrilun bana, inda ya bayyana hanyoyin da kasa da kasa za su iya bi, wajen samun tsaro a wannan zamanin da muke ciki, al’amarin dake da babbar ma’ana ga tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ya ce, kasar Sin tana son yin kokari tare da kasashen wannan yankin, tare da sauran kasa da kasa, don gina sabon tsarin tsaro a Gabas ta Tsakiya. (Murtala Zhang)