logo

HAUSA

MDD ta fitar da dala miliyan 10 domin yaki da matsananciyar yunwa a Nijeriya

2022-09-20 10:50:06 CMG Hausa

Babban asusun agajin gaggawa na MDD (CERF), ya fitar da dala miliyan 10 domin taimakawa wadanda ke fama da yunwa da tamowa a arewa maso gabashin Nijeriya.

Stephane Dujarric, kakakin sakatare janar na MDD ya bayyana jiya cewa, jami’an aikin agaji na majalisar sun jaddada cewa, idan ba a dauki mataki nan take ba, akwai yiwuwar yara sama da 5,000 za su mutu, kuma wadanda za su rayu na iya gamuwa da wata nakasa ta har abada. Yana mai cewa, tamowa ta fi yi wa yara barazanar mutuwa fiye da kwayoyin cututtuka masu yaduwa.

A cewarsa, sabon asusun na CERF, zai inganta kokarin da ake yi na ganowa tare da magance matsananciyar tamowa. Yana mai cewa a bana, yara miliyan 1.74, ’yan kasa da shekaru 5, za su iya wahala matuka saboda tamowa, yayin da sama da 300,000 za su yi fama da rashi mai tsanani na sinadaran gina jiki.  

Ayyukan masu tsattsauran ra’ayi a arewa maso gabashin Nijeriya sun raba dimbin mutane da matsugunasu, tare da jefa miliyoyi cikin matsananciyar yunwa. (Fa’iza Mustapha)