logo

HAUSA

Kasar Sin ta samu ci gaba wajen kiyaye lafiyar mata da kananan yara

2022-09-20 11:16:33 CMG Hausa

 

Lafiyar mata da kananan yara, wata alama ce da ke bayyana matsayin lafiyar al’ummar kasa, ingancin zaman rayuwar al’umma da matsayin wayewar kan kasa. Gwamnatin kasar Sin ta tanadi tsarukan kiyaye lafiyar mata da kananan yara cikin shirinta na kiyaye lafiyar al’ummar kasar Sin nan da shekarar 2030.

Alkaluma sun nuna cewa, a shekaru 10 da suka wuce, yawan kananan yara da aka bibiyi lafiyarsu ya wuce kashi 90 cikin kashi 100, kana kuma yawan mutuwar masu juna biyu da yayin haihuwa da wadanda suka haihu ba da dadewa ba, da yawan mutuwar jarirai, da kuma yawan mutuwar ‘yan kasa da shekaru 5 da haihuwa, shi ne mafi kankanta a tarihi.

Madam Song Li, shugabar sashen kula da lafiyar mata da yara na ma’aikatar lafiyar kasar Sin ta shaida wa manema labaru cewa, a cikin shekaru 10 da suka wuce, kasar Sin ta rika kyautata matsayin lafiyar mata da kananan yara, da daga matsayin samun daidaito wajen kula da lafiyarsu, kana ta yi ta kyautata tsarin ba wa mata da yara hidimar lafiya ta musamman ta ksaar Sin.

Alkaluman kididdiga sun nuna cewa, a shekarar 2021. Yawan mutuwar masu juna biyu da matan da suka haihu ba da dadewa ba, ya ragu zuwa 16.1 cikin dubu 100, kana yawan mutuwar jarirai ya ragu zuwa kashi 5 cikin kashi 1000, yayin da yawan mutuwar kananan yara ‘yan kasa da shekaru 5 da haihuwa ya ragu zuwa kashi 7.1 cikin kashi 1000, dukkansu kuma, sune mafi kankanta a tarihi.

Kasar Sin tana cikin jerin kasashe masu matsakaici da yawan kudin shiga a fannin muhimman mizanin lafiyar mata da kananan yara. Hukumar lafiya ta duniya wato WHO ta ayyana kasar Sin a matsayin daya daga cikin kasashe guda 10 wadanda suka fi samun kyautatuwar lafiyar mata da kananan yara a duniya.

A shekarun baya da suka gabata, bayan gwamnatin kasar Sin ta gyara manufofin haihuwa, yawan mata tsoffi da suka haihu ya dan karuwa. Yayin da kasar Sin ta rika kyautata lafiyar mata da kananan yara, tana himmantuwa wajen kafa tsarin ba mata da kananan yara hidimar lafiya mai salon musamman na kasar Sin, ta kuma samu ci gaba a fannonin kiyaye lafiyar yara da kuma rigakafin haihuwar jarirai nakasassu.

Yanzu akwai asibitocin mata 793 da asibitocin kananan yara 151 a kasar Sin, inda kuma ake da likitocin lafiyar mata dubu 373 da likitocin lafiyar yara dubu 206. Kana kuma akwai hukumomin kiwon lafiyar mata da yara dubu 3 da 32, inda ma’aikatan kiwon lafiyar mata da yara dubu 542 suke aiki, tare da gadoji dubu 260. Har ila yau kuma, yawan matan da suka haihu a asibiti ya wuce kaso 99 cikin dari. (Tasallah Yuan)