logo

HAUSA

Hukumar NDLEA ta Nijeriya ta kwace kg 1,855 na hodar ibilis

2022-09-20 11:09:41 CMG Hausa

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya NDLEA, ta cafke wasu mutane 4 masu safarar miyagun kwayoyi a Lagos, cibiyar kasuwnaci ta kasar, inda ta kwace kilogram 1,855 na hodar ibilis, a karshen makon da ya gabata.

Cikin wata sanarwa a jiya, hukumar ta NDLEA ta ce jami’anta sun kai samame wani dakin ajiyar kayayyaki dake yankin Ikorodu na Lagos, inda suka kwato kilogram 1,855 na hodar ibilis da darajarta ta kai dalar Amurka sama da miliyan 278.

Sanarwar ta bayyana kwacen a matsayin mafi girma na hodar ibilis kadai a tarihin hukumar. Tana mai cewa, an yi niyyar sayar da hodar da aka adana cikin manyan jakunkuna 10 da ganguna 13 ne ga masu saye a Turai da Asiya da sauran sassan duniya.

An kama mutane hudu da manajan gidan ajiyar ne bisa bayanan sirri da aikin hadin gwiwa a jihar, kuma dukkansu mambobi ne na wata kungiyar safarar miyagun kwayoyi ta kasa da kasa da hukumar take farauta tun a shekarar 2018. (Fa’iza Mustapha)