logo

HAUSA

Al’ummar Afrika ba za su taba mantawa da aminiya ta kwarai ba

2022-09-20 17:39:42 CMG Hausa

A baya-bayan nan ne kamfanonin kasar Sin suka bude cibiyar kirkire-kirkire da ilimin zirga-zirgar jiragen ruwa ta farko, a birnin Djibouti City na kasar Djibouti, da nufin inganta kirkire-kirkire na zamani da bunkasa cinikayya ta intanet tsakanin kasa da kasa.

Abun sha’awa shi ne, an kafa cibiyar ne ba don riba ba, da nufin inganta kwarewar matasa da koyar da su dabarun shugabanci da ilimin sana’o’i da dabarun tafiyar da kamfani da sauransu.

Kamar yadda aka sani, matasa su ne kashin bayan al’umma, kuma horar da matasa na da dimbin alfanu da ba zai misaltu ba. Dogaro da kai ko samun abun yi a wajen matashi, abun alfahari ne matuka, kuma zai magance kusan dukkan matsalolin da ake fama da su yanzu haka. Idan muka yi nazari, za mu gano cewa, tushen matsalolin da ake fama da su na alaka mai karfi da zaman kashe wando tsakanin matasa, don haka, da zarar matasan sun samu abun yi, wadannan matsaloli za su kau, lamarin da zai kai ga samar da ingantacciyar al’umma da ingantattun shugabanni a gobe.

Kusan duk matashin da zan gani a kasar Sin yana da sana’a, lamarin da nake alakanta shi da ci gaban da kasar ta samu da kuma zaman lafiyar da al’ummarta ke mora.

Kafa wannan cibiya ya zo a kan gaba, domin matasa da dama na da basira da tunani, sai dai ba su san yadda za su aiwatar da shi ba. Don haka, koyo daga kwararru kuma gogaggu na kasar Sin, hakika kyakkaywar dama ce ga matasan Afrika. Duba da cewa, da an kira kasar Sin a kasashenmu, abu na farko da ake tunani shi ne kasuwanci.

Bugu da kari, irin wadannan abubuwa da Sin da al’ummarta ke yi ba don riba ko wata boyayyar manufa ba, za ta taka muhimmiyar rawa wajen kyautata fahimta da kara dankon zumunci tsakaninta da kasashen Afrika, har su kasance tamkar ’yan uwa na jini a nan gaba, domin al’ummar Afrika ba za su taba mantawa da aminiya ta kwarai ba. (Fa’iza Mustapha)