logo

HAUSA

Adadin wadanda suka rasu sakamakon hadarin kwale kwale a jihar Yobe ya karu zuwa mutum 11

2022-09-20 21:23:16 CMG Hausa

Adadin wadanda suka rasu, sakamakon hadarin kwale kwalen fasinja guda 2 a jihar Yobe ya karu zuwa mutum 11. Da yake tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho, jami’in hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar NEMA reshen jihar ta Yobe Mohammed Goje, ya ce an tsamo gawawwakin mutane 11 a yankin Jumbam, na karamar hukumar Tarmuwa bayan aukuwar hadarin na ranar Asabar. Goje ya kara da cewa, baya ga mamatan, akwai kuma wasu mutum 8 da aka ceto dake samun kulawar jami’an lafiya a asibiti.

Gwamnatin jihar Yobe ta sanar da cewa, kwale kwalen 2 sun kefe ne sakamakon karfin ambaliyar ruwa da ta ci karfin su, yayin da suke kan hanyar zuwa wata kasuwa dake ci a duk mako a karamar hukumar ta Tarmuwa. (Saminu Alhassan)