logo

HAUSA

Ambaliyar ruwa ta yi sanadin mutuwar mutane a kalla 300 a Nijeriya

2022-09-20 11:15:26 CMG Hausa

Hukumar kula da agajin gaggawa ta Nijeriya (NEMA), ta ce kawo yanzu a bana, mutane a kalla 300 sun mutu sanadiyyar ambaliyar ruwa a wurare daban-daban na kasar, yayin da ake ci gaba da fuskantar ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Yayin wani taron kwararru kan ambaliyar ruwa da ya gudana jiya a birnin Abuja, darakta janar na hukumar NEMA Mustapha Habib, ya ce jihohi 29 na kasar ne suka fuskanci ambaliyar ruwa, lamarin da ya shafi mutane sama da 500,000.

A cewarsa, wasu sama da 100,000 sun rasa matsugunansu, inda suke zaune a mafakar wucin gadi, ciki har da makarantu da sauran gine-ginen gwamnati da kuma ’yan uwa.

Ya kuma shaidawa mahalarta taron cewa, wasu jihohi a yankunan arewa maso gabashi da tsakiyar kasar, na iya fuskantar ambaliya mai girma saboda hasashen da aka yi na samun ruwan sama fiye da kima, baya ga tumbatsar ruwa daga manyan madatsun ruwa dake yankunan.

Ya kara da cewa, hukumar NEMA na bibbiyar yanayin, kuma za ta duba yiwuwar kafa cibiyoyin kai daukin gaggawa domin tafiyar da ayyukan tunkarar ambaliya a jihohin dake fuskantar barazana. (Fa’iza Mustapha)