logo

HAUSA

Kasar Amurka na cin zarafin bakin haure

2022-09-20 11:05:38 CMG Hausa

Rahoton kafar watsa labarai ta FOX NEWS ta kasar Amurka a kwanan baya ya bayyana cewa, tun daga watan Oktoban bara har zuwa yanzu, wasu bakin haure 782 sun rasa rayukansu, yayin da suke neman tsallake kan iyakar kasar Mexico da ta Amurka. Jamillar da ta kasance mafi yawa a tarihi.

Dalilin da ya sa ake samun matsalar bakin haure a wannan yanki shi ne, yadda kasar Amurka ta dade tana shisshigi cikin harkokin gidan kasashen Latin Amurka. Lamarin da ya haddasa yamutsi a fannin siyasa, kana matsalar siyasar ce ta sa ake fama da koma bayan tattalin arziki, da karancin guraben ayyukan yi. Sakamakon haka, ake kwarara zuwa kasar Amurka don neman damar inganta rayuwa. A cewar Andres Lopez, shugaban kasar Mexico, idan bangaren Amurka ba ya son ganin shigar bakin haure, to, ya kamata ya taimaki kasashen dake tsakiyar nahiyar Amurka wajen raya tattalin arzikinsu. Sai dai a wannan fanni, kasar Amurka ta yi ta yin alkawura, ba tare da cikawa ba.

Ban da haka, manufar kasar Amurka a fannin kula da makaurata ita ma ta yi tasiri kan batun bakin haure. Musamman ma a lokacin da jam’iyyun siyasa na kasar ke kokarin jayayya da juna, su kan yi amfani da batun bakin haure wajen matsawa abokin takara lamba.

Ganin yadda gwamnatin kasar Amurka ke tsaurara matsalar bakin haure, gami da cin zarafin wadannan mutane, ya sa wani marubucin kasar Jean Guerrero ya ce, “kan iyakar kasar Amurka ya riga ya zama wani babban kabari.” (Bello Wang)